Continental Postal Services of Hebland

Senegal ta aike da tawaga ƙasar Guinea Bissau ƴan watanni bayan ECOWAS

A karo na farko ,wata tawaga karkashin jagoranci ministan harkokin wajen Senegal Cheikh Niang  ta kai ziyara ƙasar Guinee Bissau yan watanni bayan makamanci wannan ziyara daga ƙungiyar ECOWAS yan lokuta bayan juyin mulki.

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Tawagar da ta kumshi ministan harkokin wajen Senegal,tare da rakiyar ministan tsaro, Yankoba Diémé za su gabatar wa hukumomin riƙon ƙwarya sabon shirin sulhu, wanda ya samo asali daga taron shugabannin ƙasashen ECOWAS wanda a lokacin ne aka bukaci  Senegal ta kasance mai shiga tsakani da nufin samar da mafita bayan da ƙasar ta fuskanci juyin mulki.

 “Mun zo nan ne don gabatar da shirin sulhu da muke da niyyar aiwatarwa, da kuma cimma yarjejeniya da hukumomin riƙo kwariya  kan sharuɗɗan wannan sulhu,” in ji Ministan Senegal Cheikh Niang ga manema labarai bayan ganawa da Shugaban majalisar soji  a Guinea-Bissau, Janar Horta N’Tam.

“Mun yi tattaunawa mai amfani da Shugaba N’Tam a wannan taron.” “Ya kamata a shifuda tsarin aiwatar da wannan sulhu a cikin makonni masu zuwa, wanda zai gudana a matakai da dama, har zuwa ƙarshen tsarin zaɓe,” in ji Ministan harkokin wajen Senegal.

A haka ,ƙungiyar taECOWAS ke sa ran cimma mataki na dawo da wannan ƙasar turbar demokuradiyya da kuma dawo da tsarin mulki bayan juyin mulkin da ya hambarar da Shugaba Umaro Sissoco Embalo mai barin gado a ranar 26 ga Nuwamba, 2025.

Credit: Source link

Leave A Reply

Your email address will not be published.