‘Yan gudun hijira daga yankin Kidal na kokarin tsira daga kazamin fada da hare-haren da sojojin Mali suka tsananta kai wa mayakan JNIM da FLA yankunan Kidal da Anefis masu matukar muhimmanci, a kokarin da suke na tarwatsa mayakan da ke wurin. A cewar majiyoyin cikin gida da na jin-kai, daruruwan mutane sun kaurace wa tashe tashen hankula a yankin Tinzawatene da ke kan iyakar Mali da Aljeriya a makonnin da suka gabata, inda sojojin Mali suka tsananta yin lugudan wuta kan ‘yan tawaye.
A Gao da Ménaka, iyalan da ke sauke baki na kokarin biyan bukatun masu kwararowa
A yankin Ménaka, ‘ƴan kungiyoyin farar hula da jami’an karamar hukuma na aiki tare da ma’aikatan jin kai domin kawo musu dauki, kamar yadda Oumar Sibi Cissé, memba a majalisar gundumar Ménaka ya bayyana, yana mai cewa “Muna yawan hayar manyan motoci mu cika su da ruwan sha don kai su wuraren da wadannan ‘yan gudun hijirar suka fi yawa. Muna tattara kudade ta hanyar bayar da gudunmuwa don samar wa yara kayan makaranta ko kuma kayan tsafta.”
A cewar kungiyar agaji ta ta Mali, akalla mutane 400 da suka rasa matsugunansu sun isa Ménaka da Gao daga Kidal a cikin ‘yan kwanakin nan, domin taimaka masu, kungiyar agaji, ta samu nasarar tattara kusan biliyan daya na CFA a wajen abokan huldarta, yayin da a nashi waje ofishin jakadancin Jamus a kasar Mali ya ba da gudummawar dalar Amurka 100,000, wato kusan CFA miliyan 60. A cewar Nouhoum Maiga babban jami’in hukumar gudanarwa na kungiyar agaji ta Red Cross a Mali, tallafin ya zo a cikin yanayi na tsananin bukata inda ya ce “Yanzu a Gao, mun taimaka wa magidanta kusan 700 da kayan abinci da wanda ba na abinci ba, da kuma samar masu da matsuguni.”
Akwai bukatar karin kudi don taimaka wa ‘yan gudun hijira
Kungiyoyin agajin na ba wa ‘yan gudun hijrar tallafin kudi don su sami damar biyan bukatunsu a cikin mutunci a yankunan Kidal da kuma ci gaba da wannan aiki a Ménaka, sai dai kuma akwai karancin biyan bukatun masu hijirar in ji Nouhoum Maiga, yana mai cewa “hakan kamar bai isa ba ta la’akari da girman bukatun wadannan mutane da suka bar yankin Kidal ba tare da komai nasu ba kuma suke fuskantar matsalar rashin wadansu muhimman kayen bukatu da ke da alaka da abinci da kiwon lafiya da ilimi da bukatar duba lafiyar kwakwalwar su sakamakon tarwatsa masu tunani.“
Kungiyar agaji ta Red Cross a Mali na son duniya ta san halin da ake ciki a Ménaka da Gao
Baya ga halin da mutanen da suka rasa matsugunansu da suke samun mafaka a Gao da Ménaka, kungiyar agaji ta Red Cross a Mali na son jawo hankali kan halin kunci da fargaba da mutanen da suka yi saura a Kidal ke ciki, musamman kananan yara masu kananan shekaru da ke bukatar kula da lafiyar su da alluran rigakafin cututtuka. Miliyoyin ‘yan kasar Mali sun tsere daga gidajensu don tsira da rai a makwaftan kasashe kamar Murtaniya da Nijar sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda da kuma yawan batakashi da sojojin gwamnati ke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar JNIM da ta ‘yan tawayen Abzinawa FLA mai kokarin kwato ‘yancin gashin kan yankin arewacin Mali daga gwamnatin tsakiya.
Credit: Source link