Continental Postal Services of Hebland

Mali ta doke Sifaniya a gasar kwallon kwando a Berlin

Gasar cin kofin duniya ta mata ta kwallon kwando na ci gaba a gudana a birnin Berlin na tarayyar Jamus, inda Mali da Najeriya ke zama tawagogi biyu da ke wakiltar nahiyar Afirka. Tuni ma Mali ta ba wa marada kunya ta hanyar cimma gagarumar nasara a ranar Asabar a kan Sifaniya da ci 82-73.

Matan na Mali sun nuna kwazo a gaban Sifaniya, wacce ta zo ta biyu a gasar kwallon kwando ta kasashen Turai, alhali wakilan na Bamako sun fara shan kashi a wasansu na farko da Japan. Za ma a iya danganta nasarar ‘yan kwallon mata na Mali da ramako saboda rashin nasara da ta kai ta ratar sama da 40 a kan Sifaniya a wasan sada zumunci ‘yan kwanaki da suka gabata.

Saboda haka Mali ta zama kasa ta farko ta Afirka da ta doke tawagar kwallon kwando ta matan Sifaniya tun bayan Masar a 1950, shekaru 76 ke nan da suka gabata. ‘Yan Mali na fafata wasansu na uku kuma na karshe a matakin rukuni da Jamus, yayin da takwarorinsu na matan Najeriya ke kece raini da Faransa a wannan Litinin.

Basketball-WM der Frauen 2026 | Gruppe B | Nigeria vs. Ungarn | Ezinne Kalu spielt
Hoto: Marcin Golba/NurPhoto/picture alliance

Kasashe 16 ne ke fafatawa a babban birnin Jamus da nufin zama zakaran duniya na kwallon kwando na mata, domin maye gurbin Amurka, wacce ke rike da kambun gasar a yanzu.

A fannin kwallon kafa kuwa, Ghana ta fara wasanta na cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekara 20 da karfa hudu, inda ta sha kashi a hannun Ecuador da ci 3-0 a ranar Lahadi a Sosnowiec da ke Poland. Ecuador ta mamaye gasar a ko’ina, inda ta samu nasara sakamakon kwallayen da Rosa Flores da Domenica Arboleda suka zura. Ecuador ce ke jagorantar rukunin C.

Nahiyar Afirka ta samu wakilci daga Najeriya, Benin, Ghana, da Tanzania, inda Jamhuriyar Benin ta samu sakamako da babu yabo babu fallasa a ciki 2-2 da Mexico. Wannan na nuna cewar wakilan Afirka ba su fara tabuka wani bin a zo a gani ba, duk da ranar farko ta kasance cike da kwallaye da kuma annashuwa.

Brazil ta fara da kyakkyawan sakamako, inda ta mamaye Tanzaniya 4-1, yayin da Poland mi masaukin baki ta doke Argentina (3-0).

A halin yanzu, an hada Tanzaniya a rukunin B mai tsauri tare da Brazil, Kanada, da Ingila. Ghana za ta fafata a rukunin C tare da Faransa, Koriya ta Kudu, da Ecuador. Yayin da Najeriya da ke da kwarewa a gasar  mata take rukunin F tare da Spain, China, da New Caledonia.

Fußball-WM-Qualifikation Frauen 2026 | Österreich vs. Deutschland | Anyomi gegen Hanshaw
Hoto: Hendrik Gräfenkämper/Jan Huebner/IMAGO

Hanzu kuma sai fagen kwallon kafa, inda aka gudanar da wasannin mako na biyu na kakar-wasan Bundesliga. Sai dai abin bai zo wa Yaya-babba Bayern Munich a baibai saboda ta yi kunnen doki da Schalke 0-0 da ta yi haye babban lig kwallon kafar Jamus, lamarin da ya saukar da ita zuwa matsayi na shida.

Duk da cewa tayi nasara a wasansu na farko a gida a makon da ya gabata a kan Stuttgart da ci 5-1, amma Bayern ta yi asarar matsayinta na farko a saman teburi, inda ya koma hannun Freiburg. Rabon

kungiyar Munich ta yi wasan Bundesliga ba tare da zura kwallo ba tun ranar 25 ga Fabrairun 2025, ma’ana wasanni 47 a jere da akalla kwallo daya.

Amma a wasanta da, Bayern Munich ba ta sanya taurarinta biyu, Harry Kane da Michael Olise a cikin ‘yan wasa 11 da suka fara wasa ba. Wai shin sabanin yadda ta saba, raina Schalke ne ya sa Bayern yin sako-sako a wasan? A lokacin da yake amsa wannan tambaya, kocin Vincent Kompany ya ce sam abin ba haka yake ba:

Fußball-Bundesliga 2012/13 | Borussia Dortmund vs. FC Schalke 04 | Höwedes gegen Lewandowski
Hoto: Elmar Kremser/Sven Simon/picture alliance

“Game da rashin Kane da Olise, da farko dai shawara ce mai ma’ana. Wadannan ‘yan wasa biyu sun shiga cikin tawaga a makare. Tabbas, ba za mu iya tilasta musu su buga kowane wasa gaba daya ba. Kuma wasan da suka yi da Osnabrück a gasar cin kofin kalubale na Jamus ya jefa mu cikin mawuyacin hali, kuma wasa ne mai muhimmanci ga sauran gasar. Na kwana da sanin cewa wasa da Schalke ba zai yi sauki ba, amma fifikon a gare mu kamar yadda na ce, shi ne wasan da Osnabrück, wasan da ake yi cire ka kai tsaye a gasar cin kofin Jamus.”

A yayin da Bayern Munich ta yi tuntube, ita kuwa abokiyar hamayyarta Borussia Dortmund ta samu nasara mai mahimmanci a kan TSG Hoffenheim da ci 3-2, lamarin da ya sanya ta a matsayi na uku da maki shida.

Ita kuwa Bayer Leverkusen ta huce haushinta a kan Union Berlin da ci 4-0, mako guda bayan da sabon shiga Elversberg ta doke su a ranar farko.

Game da sauran sakamakon da aka samu a wasan mako na 2 na Bundesliga kuwa, RB Leipzig ta sha kashi da ci 3-1 a hannun Bremen, yayin da sabon shiga Elversberg ta doke Borussia Mönchengladbach da ci 4-3, ita kuwa Stuttgart ta doke FC Köln da ci 4-1, yayin da Augsburg ta samu nasara da ci 4-1 a kan Frankfurt.

Bayan wasan mako na 2, FC Augsburg tana jagoranci teburin da maki 6, kuma tana da bambancin kwallaye mafi girma (+6) idan aka kwatanta da Freiburg, Dortmund, da Elversberg, wadanda suma ke da maki 6 kowacce.

Idan muka leka fagen La Liga na Sifaniya kuwa,  ta doke Valencia da ci 5-0 a ranar Lahadi, inda Lamine Yamal ya zura kwallaye biyu. Wannan shi ne karo na uku a cikin wasanni hudu da ‘yan wasan da Hansi Flick ke horaswa suka zura kwallaye 5 a wasa daya, bayan nasarar da suka samu da ci 5-0 a wasan farko da Elche. Sannan kungiyar ta yankin Kataloniya ta yi amfani da rashin nasarar abokan hamayyarta Real Madrid da Atlético Madrid wajen darewa saman teburi lig na kwallon kafar Sifaniya.

UEFA Champions League 2014/15 | Finale | Juventus Turin vs. FC Barcelona in Berlin
Hoto: Cosmin Iftode/Depositphotos/IMAGO

A Jamhuriyar Nijar, a Daidai lokacin da ya rage kimanin watanni bakwai a gudanar da zaben shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA, masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a kasar sun bayyana aniyarsu da bin sahun wasu kasashen Afirka wajen kawo goyon baya ga takarar shugaban hukumar ta FIFA na yanzu Giani Infantino a zaben na tafe. Wannan na zuwa ne a daidai loakcin da Hukumar kwallon kafa ta Turai wato UEFA da wasu kasashen na duniya ke nuna adawarsu da yinkurin tazarcen shugaban na hukumar FIFA wanda suke zargi da yin gaban kansa wajen tafiyar da hukumar da daukar wasu matakai da ka iya haifar da komabaya ga ci gaban kwallon kafa a duniya. Wakilinmu a Yamai Gazali Abdou Tasawa ya duba mana wannan batu, ga kuma rahoton da ya aiko mana””.

Dan Italiya Kimi Antonelli na kungiyar Mercedes ya lashe gasar tseren motoci ta Formula 1 ta Italiya a Monza ranar Lahadi, inda ya ba abokan hamayyarsa mamaki a fafatawar neman lashe gwani na gwanyen duniya.

Duk da cewa ya fara tseren a matsayi na 19, amma direban mai shekaru 20 ya yi rawar gani, lamarin da ya ba shi damar zama dan Italiya na hudu da ya yi nasara a cikin shekaru 60.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manaima labarai bayan tseren, Antonelli ya ce”Bai yi tsammanin wannan nasarar ba, abin mamaki ne, saboda haka ina matukar farin ciki. Mafarki ne ya cika. Na yi tunanin samun matsayi mai kyau, amma ba nasara ba,” in ji Antonelli.

Credit: Source link

Leave A Reply

Your email address will not be published.