Jami’an tsaro a Liberia sun sanar da kama hodar iblis da aka bayyana cewa shi ne kame mafi girma da aka taɓa yi cikin tarihin ƙasar.
Wallafawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
Babban Sufeton Ƴansandan ƙasar Gregory Coleman ya ce binciken da suka gudanar da bayan gano ƙunshi wasu abubuwa da ake zargin cewa miyagun ƙwayoyi ne a wani gida da ke unguwar Duazon kusa da birnin Monrovia fadar gwamnatin ƙasar ne ya tabbatar da cewa hodar ibilis ce da ƙimarta ta kai dalar Amurka milyan 370.
An cafke mutane da dama da ake zargin cewa suna da hannu a fataucin wannan ƙwayar, inda ake ci gaba da faɗaɗa bincike dangane da lamarin da ya yi matuƙar tayar da hankula lura da adadin wannan hodar.
A ƙarin bayanin da ya yi wa manema labarai, Sufeton Yansandan ya ce ‘’bayan samun bayanai dangane da wani gungun fataken miyagun ƙwayoyi da ke da muguwar manufa a cikin ƙasar ne suka ƙaddamar da bincike, inda daga bisani suka yi nasarar gano hodar da kuma wasu mutanen da ake zargi da hannu a safarar.’’
Alƙalamu na nuni da cewa tsakanin 2018 zuwa 2023 an samu ƙaruwar fataucin miyagun ƙwayoyi a wannan ƙasa da ke Yammacin Afirka, yayin da bayanai ke cewa daga cikin mutanen da aka kama a wannan karo har da waɗanda ke ɗauke da fasfo na kasar Spain da kuma na Colombia.
Credit: Source link