Continental Postal Services of Hebland

Burkina Faso ta bai wa ‘yan jarida horon soja

‘Yan jarida 44 maza da mata ne suka halarci horon na kwanaki shida da aka gudanar a makarantar ‘yan sanda da ke kusa da birnin Ouagadougou, inda aka gan su sanye da kayan soja tare da rike bindigogi.

Ministan yada labarai kuma kakakin gwamnati, Pingdwende Gilbert Ouedraogo, ya ce dan jarida da ba shi da kishin kasa barazana ne ga kasarsa.

Karin bayani : Sojojin Intanet a Burkina na wa ‘yan jarida barazana – RSF

Matakin na zuwa ne a karkashin gwamnatin Kyaftin Ibrahim Traore, wadda ta dakatar da wasu kafafen yada labarai, yayin da kasar ke ci gaba da fama da hare-haren kungiyoyin masu ikirarin jihadi.

Karin bayani : Yaushe ‘yan jarida za su samu ‘yanci a AES?

Credit: Source link

Leave A Reply

Your email address will not be published.