Continental Postal Services of Hebland

Yadda al’umomi a jihar Neja ke gudun hijira a Jamhuriyar Benin saboda ƴanbindiga

Asalin hoton, NPF

Bayanai daga yankin karamar hukuma Borgu ta jihar Neja, sun ce jama’ar garuruwa da dama na yin gudun hijira zuwa garuruwan wasu jihohin kasar, har ma da tsallakawa zuwa makwabciyar kasar, jamhuriyyar Benin, inda suka sami mafaka don guje wa hare-haren ‘yan bindiga.

Hakan na faruwa ne duk da matakan da hukumomi ke cewa suna ɗauka domin tabbatar da tsaro a yankin.

Wani mazaunin daya gada cikin garuruwan da ke kan iyakar Najeriya da jamhuriyyar Benin, ya yi wa BBC bayani kan wannan mawuyacin hali da ya ce suna ciki:

”To ba ka da gida an kone, ba ka da gona an hana ka noma, to ya za ka yi da rayuwarka? Ka ga dole ka kaura.”

Gudun hijirar da jama’ar garuruwan ke yi dai ta samo asali ne daga gagarumin hari na baya-bayan nan da ‘yan bindiga suka kaddamar a wasu garuruwa, in ji mutumin yankin:

Credit: Source link

Leave A Reply

Your email address will not be published.