Continental Postal Services of Hebland

Tawagar Nijar ta gana da hukumomin Benin a Kwatanu kan batun buɗe iyakokinsu

A jiya juma’a ce tawagar jamhuriyar Nijar dauke da ta hada da ministoci da mashawartanm shugaban ƙasa Tiani ta isa Kwatanu domin ci gaba da tattaunawa da hukumomin Benin game da sake buɗe iyakokin da suka raba, wanda aka rufe a gefen Nijar tun watan Agusta na 2023. Wannan sabon matakin tattaunawa wani bangare ne na sulhun da Shugaba Romuald Wadagni da Abdourahamane Tiani suka fara da nufin daidaita dangantakar ƙasashen biyu.

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

 

Tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu wato Jmahuriyar Benin da Nijar na ci gaba da gudana a kan tsarin ganin an sake buɗe iyakokin da suka raba. Ministan Harkokin Cikin Gida, Janar Mohamed Toumba,wanda ke jagorantar tawagar ta isa Kwatanu da yammacin Juma’a don shiga zagaye na biyu na tattaunawar da aka sadaukar domin sake bude iyakokin da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Balaguron tawagar zuwa jamhuriyar Benin ya biyo bayan gabatar da rahotannin da kwararrun ƙasashen biyu suka  yi a karshen wannan mako ga shugabanin ƙasashen biyu Romuald Wadagni da Abdourahamane Tiani.

Tun bayan hawansa kan mulki,Shugaban Benin Romuald Wadagni ya sanya daidaita dangantaka da Nijar a matsayin fifiko na diflomasiyya.

Ziyararsa zuwa Yamey a ranar 2 ga Yuni, inda Janar Abdourahamane Tiani ya karɓe shi, ta taimaka wajen sake fara tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu.

Tun daga wannan taron, kwararru daga Benin da Nijar suna aiki tare don fayyace yanayin sake buɗe kan iyakar cikin sauki.

Credit: Source link

Leave A Reply

Your email address will not be published.