Continental Postal Services of Hebland

Rikicin siyasar Senegal ya dauki sabon salo

Shugabannin kungiyoyin farar hula da ‘yan jarida na shan gargadi game da barazana da ke wakana a fagen siyasar Senegal, bayan raba gari da aka yi tsakanin Shugaba Diomaye Faye da kuma firaministansa Sonko.

Hasali ma dai, ‘yan ganin kashe nin Pastef jam’iyya mai mulkin Senegal, suna amfani da shafukan sada zumunta wajen  kare gwaninsu tare da shafa kashin kaji ga masu suka ko masu adawa da manufofin Ousmane Sonko.

Siyasar ta shiga rudani

Senegal Dakar | Shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal (a hagu) da shugaban majalisar dokoki Ousmane Sonko (a dama)
Shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal (a hagu) da shugaban majalisar dokoki Ousmane Sonko (a dama)Hoto: Cem Ozdel/Anadolu/picture alliance

Sai dai wannan na barazana ga ‘yancin fadan albarkacin baki da Senegal ta yi fice a kai, saboda ‘yan adawa na taka-tsantsa kan kalaman da suke furtawa saboda tsoron daukar fansa daga bangaren fitaccen dan siyasan.

Tun bayan da ya dare kan kujerar jagorancin majalisar dokokin Senegal, tsohon firayiminista Ousmane Sonko ya yi barazanar ga kafofin watsa labarai: inda ya ce ba za su kara barin kafofin watsa labarai su rubuta duk abin da suke so game da mutane ba, da sunan abin da ake kira ‘yancin ‘yan jarida, ba tare da dogara kan wata majiya mai tushe ba.

Ousmane Sonko na yawan bayyana tababa game da sahihancin tsarin shari’a na Senegal. Ko a  watan Nuwamba na 2025, a lokacin Ousmane Sonko na rike da mukamin firaminista, ya yi Allah wadai da cikas da wasu alkalai ke kawowa ga badakalar binciken kudaden da aka yi saman da su, wanda a cewarsa tsohon tsarin gwamnatin da ta shude ke ci gaba da katutu. Sai dai kalaman da yake amfani da su wajen  nesanta kansa daga tsarin shari’ar na tayar da hankalin alkalai.

Batun kare hakkin mata:

Senegal Dakar 2026 | Rikicin siyasar Senegal
Rikicin siyasar Senegal ya dauki sabon saloHoto: DW

A daya hannu kuma, duk da cewa mata na yin Allah wadai da koma baya da suka samu a fannin kare wasu hakkokinsu, amma kalilan daga cikin suke iya sukar Ousmane Sonko. Amma Ossama Monique Sagna, wata mai fafutukar kare hakkin mata ta Senegal, na sahun wadanda sue iya fitowa don yin tir da rashin amfani da dokar daidaiton jinsi da ta fara aiki tun 2010 a kasar Senagal.

Gwamnatin da ta gabata ta tsohon shugaban kasa Macky Sall ta kunshi mata bakwai, yayin da ta Ousmane Sonko da ta shude a makon da ya gabata ta kunshi mata hudu ne kacal, ma’ana kusan kashi 13% na yawan minitoci. Wannan ya haifar da muhawara da suka, da rashin gamsuwa a tsakanin jama’a.

Alkaluman baya bayan nan sun nuna cewar an samu rahotannin kisan gilla 18 da aka yi wa mata a shekarar 2025. Sai dai, masu fafutukar kare hakkin mata sun yi imanin cewa adadin ya fi haka saboda rashin samun cikakken kididdiga a hukumance.

Credit: Source link

Leave A Reply

Your email address will not be published.