Wannan ganawar dai, na zaman matakin karshen na aikin kwamitin da aka kafa a yayin ziyarar sabon shugaban kasar Benin a birnin Yamai. Saidai kuma, gwamnatin mulkin sojan Nijar ta gindaya wasu sharudda kafiun a kai ga bude iyakokin. Wata tawaga ta ya da zango a kasar Bénin a karkashin jagorancin ministan harakokin cikin gida na Nijer Janar Toumba Mohamed Boubacar.
#b#Tuni dai ‘yan kasar, ke bayyana ra’ayoyinsu mabanbamta a kan batun. Alhaji Abdul-wahab Abdul Nasir wakilin kungiyar masu manyan motocin dakon kaya da ke zaune a kasar Bénin ya shaidawa wakilinmu ta wayar tarho cewa, dole ne kasashen biyu su aza sharudda kuma wajibi ne sai kowa ya ciza ya kuma saki idan ana bukatar cimma daidaito. A bun jira a gani dai shi ne, yadda hukumomin Benin za su karbi sharudda da gwamnatin mulkin sojin ta gindaya kamun a kai ga bude iyakokin.
Credit: Source link