Kaciya ko yanke matuncin mace al’ada ce da dokokin kasar Guinea suka haramta, sannan kuma suka tanadi hukunci mai tsauri a kai. Sashe na 258 na kundin shari’ar kasar da ke Yammacin Afirka, ya haramta aikata duk wani nau’i na yankewa ko cire wani bangare na matucin mata. Hasalima sashe na 259 na dokokin Guinea ya tanadi hukuncin dauri a gidan yari da zai iya kai wa shekaru biyar, tare da cin tarar miliyan uku na kudin kasar kwatankwacin Euro 300.
Lokacin hutu ga ‘yan makaranta, ko na tashin hankali?
Idan kaciyar ta yi sanadin rayuwa, masu hannu a cikin aika-aikar ka iya fuskantar hukuncin daurin shekaru biyar zuwa 20 kamar yadda sashe na 261 na kundin dokar ya tanadar. Sai dai duk da wadannan matakai na doka, yayin hutun ‘yan makaranta kungiyoyin kare hakkin mata a Guinea sun tashi haikan wajen sanya ido sosai saboda a wannan lokaci ne ake fara kakar yi wa ‘yan mata kaciya kuma galibi ana yin ta ne a boye. To amma babbar damuwa ita ce, a wasu lokutan illolin kaciyar na kasancewa masu matukar muni da kuma hadari ga ‘yan mata.
Ko da a shekarar da ta gabata, an samu mutuwar wata yarinya karama a yankin Kudu maso Gabashin Guinea, bayan aikata wannan al’ada. Shugaban kungiyar kare hakkin mata ta ”Femmes Développement et Droits Humains Moussa Yéro Bah ya ce, har yanzu tabon wannan danyen aiki bai gama shafewa daga zukatan mutane ba. To amma duk da cewa a wasu lokuta doka na aikinta ba sani ba sabo, Mussa Bah ya bayyana takaici kan yadda wadansu masu aikata al’adar kaciyar ke yin abinsu ba tare da sanin ‘yan doka ba.
Babu macen da ta tsira daga al’adar yin kaciya
Babban abin tashin hankali ma a Guinea shi ne, kasancewa kaciyar matan ba ta bar yaro ba kuma ba ta bar babba ba batu ne da ya shafi kowane rukunin shekarun mata. Sau tari ana yi wa mata kaciya ne, domin martaba al’adun gargajiya. To amma kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin mata na dogaro da wayarwa jama’a kai da kuma fatan samun karin kwarin gwiwa daga hukumomin gwamnati wajen aiwatar da doka, domin taka birki ga wannan al’ada da ka iya haifar da mummunar illa ga lafiyar kanana ‘yan mata.
Fassara: Mohamed Tidjani Hasane
Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja’afar
Credit: Source link