Continental Postal Services of Hebland

Guinea Bissau: Zaben raba-gardamako dakile adawa?

Sakamakon wucin gadi na zaben ya nuna kaso 70 cikin 100 na wadanda suka kada kuri’ar raba-gardaman ta Guinea Bissau, sun amince da sabon kundin tsarin dokar da ya tanadi canza kundin tsarin mulkin kasar daga na mai ruwa biyu zuwa na shugaban kasa mai cikakken iko. Hakan na nufin da zarar kotu ta tabbatar da sakamakon, kasar za ta koma kan tsarin shugaba mai cikakken iko da zai iya nada wa da cire firaminista da mambobin gwamnati da ma ikon rushe majalisar dokoki.

Rage kashe kudin kasa ko dakile’yan adawa?

Wani babban sauyi da sabon kundin tsarin mulkin ya tanada shi ne, rage adadin kujerun ‘yan majalisar dokoki daga 102 zuwa 65 da kuma yawan gundumomi daga 29 zuwa 12 da nufin rage kashe kudin kasa. To sai dai ga wasu masanan siyasar kasashen yammacin Afirka kamar Mamadou Sy Albert na kasar Senegal, wannan mataki babu abin da zai haifar sai kara rikita fagen siyasar kasar ta Guinea Bissau.

Afirka: Kokarin dakile ‘yan adawa

To view this video please enable JavaScript, and consider upgrading to a web browser that supports HTML5 video

A hannu guda, wannnan sabon kundin tsarin mulki na iya zama wani babban kalubale ga wadanda ke son tsayawa takara a nan gaba. Dole ne duk mai son yin takarar shugaban kasa ya biya milyan 50 na CFA a matsayin kudin takara, kwatankwacin dalar Amurka 90,000. Haka kuma duk jam’iyyun da ke son marawa dan takara baya, dole sai sun samu goyan bayan mambobinsu 5,000 tare da mambobi 300 daga duk jiha daya. 

Juyin mulki na ban mamaki?

A ranar 26 ga watan Nuwamban 2025 ne, sojoji suka hambarar da gwamnatin Umaro Sissoco Embalo karkashin jagorancin babban hafsan sojan kasar Janar Horta Inta-A Na Man a wani juyin mulki da ke zama karo na biyar a kasar tun daga shekara ta 1980. Juyin mulkin dai mai cike da rudani, ya wakana ne a daidai lokacin da ake sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar.

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja’afar

Credit: Source link

Leave A Reply

Your email address will not be published.