Daukacin mambobi 59 na majalisar dokokin Burkina Faso ne suka amince da dokar da ta shafi ‘yancin addini a kasar. A lokacin da yake nuna goyon bayansa ga dokar, Emile Zerbo, ministan cikin gida na Burkina Faso ya ce an samar da ita ne da nufin cike gibin da ke akwai a game da al’amuran da suka shafi addini da kuma yaki da tsattsauran ra’ayin Musulunci da ya kunno kai a kasar.
“Mutane na fakewa da ‘yancin addini don kunna wutar rikici a kasar ta hanyar yada wa’azin tsaurin ra’ayi, wa’azin da ke da wahalar karbuwa a kasar da ke karkashin ikon doka. Wannan sabuwar dokar da aka amince da ita za ta taimaka wajen yaki da tsaurin ra’ayin addini kuma za ta ba da damar tantance duk wadanda suke shigowa kasarmu don yin wa’azi a wuraren ibada.“
Sabuwar dokar ta kunshi wasu matakai da za su daidaita ayyukan addini, imma Kiristanci ne ko Musulunci ne ko addinin gargajiya. Wadannan matakan sun hada da sakar wa kowa marar gudanar da addinin da yake so, da tsara yadda za a gudanar da wa’azi, da tantance hanyoyin da kungiyoyin addinai ke samun kudi, da kuma yaki da kalaman batanci da kiyayya.
Sai dai, daya daga cikin matakan da ya tanadi haramta gina wuraren ibada a gine-ginen gwamnati, ya jawo suka mai tsauri musamman a shafukan sada zumunta. Wasu shugabannin addinai suna daukar wannan a matsayin da ya mayar da hannu agogo baya game da tsarin yin addini a wuraren da gwamnati ke da iko a kansu ciki har da jami’o’i da sauransu. Sannan nuna damuwa game da yiwuwar takaita ayyukan addini. Sai dai ministan cikin gida na Burkina Faso Emile Zerbo, ya ce ba haka lamarin yake ba.
“Ba a haramta yin sallah ba, amma abin da aka haramta shi ne, kebe wani wuri na gwamnati don ba shi fasali na addini, alhali kuwa ba manufar gine-ginen gwamnati ba ne. Wannan doka ba a yi ta don yakar addinai ba, kamar yadda wasu suka yi ikirari. Wannan doka ba za ta faranta ran wadanda ke son rikici ba. Wasu da gangan suka jirkita abin da aka rubuta.”
Wannan sabuwar dokar addini ta tanadi cewa daga yanzu, ana bukatar izinin gwamnati kafin a bude wurin ibada. Sannan wadanda aka riga aka gina su na da wa’adin shekara daya don a yi musu rejista. Kazalika, dole ne masu wa’azi da limamai da wadanda ke da alhakin kula da wuraren ibada su nuna takardun da ke tabbatar da cancantarsu a fannin addini. Bugu da kari, dole ne kungiyoyin addinai su bude asusunsun ajiyar kudadensu a Baitulmali, da ke zama cibiyar gwamnatin Burkina Faso.
Amma kafin a amince da dokar, an tattauna wasu tanade-tanadenta da shugabannin addinai, da aka gayyata domin su bayyana matsayarsu. Wadannan shugabannin sun nuna shakku game da wasu hukunce-hukunce, ciki har da daurin shekaru biyar a gidan yari ga wanda ya saba dokar, lamarin da ya sa a karshe aka yi watsi da ita.
Tun a shekarar 2012 ne aka ba da shawar kafa dokar addinai, a lokacin da aka gudanar da babban taron tattaunawa kan tsarin addini. Hasali ma dai, an gabatar da kudurin dokar ‘yancin addini a majalisar dokokin Burkina Faso a shekarar 2016 kafin a janye ta da nufin fara tattaunawa da shugabannin addinai. Sannan a shekarar 2023, bayan da aka gano gibin da ta kunsa, sabbin hukumomin mulkin soji sun yi mata kwaskwarima domin ta dace da kalubalen tsaro da ake fuskanta.
Amma ita sabuwar dokar na da nufin inganta tsarin addini, ko da yake tana haifar da damuwa game da yiwuwar takaita ‘yancin addini. Saboda haka, mataki na gaba mai sarkakiya zai kasance na aiwatar da ita a tsakanin mabiya addinai daban daban.
Credit: Source link