Continental Postal Services of Hebland

An yanke wa ɗan jaridar Mali hukuncin ɗaurin shekaru 2 saboda sukar gwamnati

A Mali, an yanke wa wani ɗan jaridar ƙasar hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, biyo bayan kalaman da ya yi cikin wani shiri a gidan talabijin game da halin da tsaron ƙasar ta yammacin Afrika ke ciki.

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Abderhamane Keita, babban editan jaridar Le Temoin ne a Mali, kuma an kama shi tun watan Yunin da ya gabata, saboda zarginsa da zagon ƙasa ga haɗin kan ƙasar, baya ga wallafawa da kuma yaɗa labaran ƙarya a kan gwamnati.

An kama ɗan jaridar ne bayan kalaman da ya yi a cikin wani shiri na gidan talibijin, wanda ya mayar da hankali akan matsalar tsaro da birnin Kidal na arewacin Mali ke fuskanta, kuma ya ce yana ƙarƙashin ikon jagoran ƙungiyar mayaƙan JNIM.


Ɗan jaridar Mali, Abderahmane Keïta © RFI

Keita ya bayyana gaban sashen kula da laifuffukan intanet na ƙasa a makon jiya, gabanin sanar da yanke masa hukunci a ranar Litinin.

Lauyansa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, za su ɗaukaka ƙara game da hukuncin da aka yanke wa ɗan jaridar.

Tuni ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa da ƙasa wato Reporters Without Borders ta kira hukuncin a matsayin rashin adalci, da kuma wani sabon salon na mayar da aikin jarida laifi.

Credit: Source link

Leave A Reply

Your email address will not be published.