Jami’an gabar teku sun gano gawarwakin wasu baƙin haure 15 a gaɓar tekun Libya waɗanda aka yi tsammanin sun fara tafiyarsu zuwa Turai, a makon da ya gabata.
Wallafawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
Jirgin ya kife ne da mutane 61, kamar yadda wasu mutane 10 da suka tsira daga cikin jirgin suka shaidawa jami’ai.
Rahotanni sun bayyana cewa baya ga waɗannan mutane an gano wasu daban a yankin Tobruk gab da iyakar Masar, kuma gawarwakinsu sun ruɓe ta yadda ba’a iya ganesu, kana mahukunta sun ce akwai yiwuwar a gano ƙarin wasu gawarwakin.
Wasu hotuna da jami’an bayar da agaji na Red Crescent da ke aiki a Tobruk suka wallafa a shafinsu na Fcebook sun nuna masu ceto sanye cikin fararen kaya na tsamo ruɓaɓɓun gawarwaki, tare da sanyasu cikin ledojin adana gawa.
Tun bayan hamɓarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a 2011 Libya ta zama wata hanyar ratsewar baƙin haure zuwa Turai daga Afrika,sakamakon rikice-rikice, tsananin talauci, sauyin yanayi da sauransu.
Credit: Source link