Amurka ta dawo da wasu bakin haure 10 ƴan asalin ƙasashen Ghana, Liberia, Benin, Nigeria, da Togo zuwa Saliyo a jiya juma’a,wanda yawan su a wannan lokaci ya kai 32, kamar yadda gwamnati ta sanar a yau asabar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
Dawo da wadanan mutane na zuwa ne a wani lokaci da shugaban Amurka Donald Trump ya ci gaba da shirin sa na korara bakin haure a duk ida suke cikin wannan ƙasa ta Amurka.
Amurka na kwashe bakin haure marar sa takardu daga cikin gida Amurka zuwa ƙasashe uku.
Wannan rukuni na uku na ‘yan ƙasashen uku ya kunshi ‘yan Ghana shida, daya daga Liberia, daya daga Benin, daya daga Najeriya, daya daga Togo, wadanda suka isa ranar Juma’a a filin jirgin saman Freetown, a cewar wata sanarwa da gwamnati ta fitar a yau asabar ga AFP. Mutanen sun hada da maza tara da mace daya.
Wadannan sabbin bakin haure sun kawo adadin bakin haure 32 da Amurka ta kora zuwa Saliyo, bayan mutane 22 da aka tura a baya a kungiyoyi biyu daban-daban.
Sierra Leone na daga cikin ƙasashen Afrika da ke fama da talauci,a yammacin Afirka, ita ce ta baya-bayan nan da ta shiga jerin kasashen Afirka da suka amince a cikin ‘yan watannin nan su karbi mutanen da aka kora daga Amurka, ciki har da Equatorial Guinea, Ghana, Rwanda, Sudan ta Kudu, Kamaru, Eswatini, da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. Waɗannan yarjejeniyoyi galibi sun haɗa da tallafin kuɗi ko na kayan aiki daga Amurka.
Wasu ƙasashe, kamar Jamhuriyar Demokraɗiyyar Congo (DRC), sun yi maraba da baƙi daga wasu nahiyoyi, kamar Latin Amurka.
Amurka za ta ba da kuɗin shirin a Saliyo na dala miliyan 1.5 (€1.3 miliyan) “don biyan kuɗin agaji da ayyukan da suka shafi wannan yarjejeniya,” a cewar wata takarda daga ma’aikatar Harkokin Waje ta Saliyo da AFP ta gani.
Credit: Source link