Continental Postal Services of Hebland

Ƴan farar hula sun soki shirin Mali da Chadi da Burkina Faso na ficewa daga ICC

Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula da ƴan siyasa a ƙasashen Burkina Faso, Mali, da Chadi sun soki matakin gwamnatocinsu na ficewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya ICC sakamakon zarginta da rashin adalci a shari’un da take yi da kuma nuna wariya wajen kamawa da kuma yanke hukunci.

Wallafawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Wannan kira na zuwa ne yayin wani taron muhawara da aka shirya kan wannan batu a birnin Paris don lalubo hanyoyin da za’a bi wajen shawo kan ƙasashen su koma cikin wannan kotu.

Taron ya samu halartar manyan lauyoyi, yan siyasa, yan kungiyoyin fararen hula daga ƙasashen Ƙawancen Sahel (AES) da Chadi, kuma mahalarta sun nuna adawa ƙarara da matakin ƙasashensu na ficewa daga ICC.

Ƙasashen dai sun ayyana irin tasirin da Amurka ke da shi a wannan kotu da kuma yadda take murɗa shari’a da kuma nuna fifiko kan son kai game da wanda za’a kama ko kuma wankewa a wannan kotu a matsayin babban dalilin ficewar su.

A tsakiyar watan Yulin da ya gabata, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana aniyarsa ta “wargaza ICC”, sai dai yayin taron Tahir Korom, shugaban ƙungiyar Young Progressives of Central Africa, ya ce ficewar waɗannan ƙasashe daga ICC ya fi alaƙa da ƙoƙarin guje wa hukuncin shari’ar kotun a kansu ba wai kishin ƙasashensu ba.

Credit: Source link

Leave A Reply

Your email address will not be published.