Wani bincike da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta fitar ya bayyana cewa, sauyin yanayi da ya haifar fari ya tilasta wa dubban mutane a ƙasar Angola tserewa zuwa maƙwabciyarsu Namibia don neman tsira, abin da ya raba iyalai da dama da muhallansu, inda mafi yawancin waɗanda abin ya shafa mata ne da ƙananan yara waɗanda ke cikin mawuyacin hali.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
A cewar ƙungiyar, waɗannan mutane na tserewa ne sakamakon ƙarancin abinci, ruwan sha, da kuma rushewar bangaren noma da kiwo da suka dogara da su a yankunansu na asali.
Sai dai, maimakon su sami mafaka da agajin jinkai a Namibia, rahoton ya nuna cewa suna fuskantar matsananciyar rayuwa da kuma nuna musu bambanci a sansanonin da suka fake.
Amnesty International ta yi tir da yadda hukumomin ƙasar Namibia ke gudanar da bincike da kuma yanke wa waɗannan ‘yan gudun hijira hukunci mai tsanani.
Rahoton ya jaddada cewa ana tsare da da yawa daga cikinsu a cikin mummunan yanayi, wanda hakan ke keta ƙa’idodin kare haƙƙin ɗan adam na ƙasa da ƙasa.
Bugu da ƙari, ƙungiyar ta bayyana damuwa kan yadda ake tilasta wa waɗannan mutane komawa ƙasarsu ta Angola ba tare da tabbatar da tsaronsu ko samar musu da madadin mafaka ba.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Namibia da ta dakatar da duk wani shiri na korar mutanen, kuma ta ba su kariya kamar yadda dokokin duniya suka tanada, tare da neman gwamnatin Angola da ta ɓullo da tsare-tsare masu dorewa don taimaka wa al’ummomin da sauyin yanayi ya daidaita.
Abin da masana ke cewa a yanzu shine, sauyin yanayi ba barazana ba ce kawai ga muhalli, babban dalili ne da ke rura wutar kalubalen jinkai da hijira a yankin Kudancin Afirka.
Credit: Source link