Wannan taro ya hada kasashe mambobin kungiyar ta AES da aminansu da sauran abokan hulda, domin tattauna batutuwan da suka shafi kwance damarar mayaka da wargaza kungiyoyinsu da gyaran hali da kuma sake shigar da tsofaffin mayaka na yankin Sahel cikin tsarin rayuwa ta yau da kullum. Shiri wani bangare ne na neman tabbatar da tsaro ga al’umma da samar da zaman lafiya ga kasashen da kuma kara jajircewa, wajen karfafa tsarin samar da cikakken mulkin kai na kasashen yankin na Sahel.
Bai wa batun tsattsauran ra’ayi muhimmanci?
A jawabin da ya yi kwamishinan ‘yan sanda Janar Ayouba Abdourahmane ya bayyana cewa, idan ana nazarin matsalolin tsaro a Nijar da ma yankin sahel dole a duba batun masu tsattsauran ra’ayi na wasu kungiyoyin addini da kuma amfani da ake da sojojin haya daga kowane bangare na duniya ta hanyar wasu manyan kasashe da ke da akidar ci gaba da mulkin mallaka da nufin ganin sun wargaza tsarin ci-gaba da kasashen yankin suka sanya a gaba.
An samu halartar kwararru na kasashen AES da sauran kasashe abokan hulda, kuma a cewar farfesa Dicko Abdourahamane daya daga cikin masu halartar taron tsarin da aka kira DDR yana da matukar muhimmanci. Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai Kula da Ci-gaba PNUDD na daga cikin masu goyon bayan wannan babban taro, wanda a cewar wakiliyar hukumar a Nijar Jane O Yeboh hukumomin kasar sun cancanci yabo dangane da tsara wannan taro.
Ko tsarin janyo hankali zai zamo mafita?
Wannan tsari dai da aka kira na DDR, na nuni da shawarwarin da masana harkokin tsaro da ayyukan ta’addanci ke bayarwa tare da jan hankalin magabata na cewa shi fa yaki da ta’addanci ba wai sai da tsinin bindiga ba kamar yadda Farfesa Dicko Abdourahamane ya yi tsokaci a kai. Taron na daga cikin tsarin samar da zaman lafiya da kasashen na AES suka sa a gaba, wanda kuma Jamhuriyar Nijar ta yi suna a fannin sulhu da janyo hankalin mayaka na su ajiye makamansu su shiga a yi ayyukan gyaran kasa tare maimakon tayar da zaune tsaye da babu riba a cikinsa.
Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja’afar
Credit: Source link