Yayin da ake ci gaba da samun matsalolin tsaro na masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel, gwamnatin Burkina Faso ta amince da ƙudirin doka na ɗaukar ƙarin sojoji dubu ɗari, matakin da ke fuskantar suka daga ƙungiyoyin kare haƙiƙin ɗan’adama game da yadda jami’an tsaron ƙasar ke take hakkin bil Adama.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
A cikin wani rahoto da ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta fitar makwanni uku da suka gabata, ta ce Burkina Faso na shirin sake ɗaukar tsoffin sojoji dubu 50 da kuma sabbi da basu taɓa aikin soja ba suma 50, don kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke damun ƙasar.
Ƙungiyar ta zargi sojojin Burkina Faso da kuma ƴan bangar da ke taimaka musu na VDP, ke aikata laifukan cin zarafi, wani lamari da kai tsaye ke suka kan sanarwar da ministan tsaron ƙasar Janar Simpore ya yi game da ɗaukar sabbin jami’an tsaron.
Wannan mataki dai ya zo ne dai-dai lokacin da gwamnatin Ouagadougou ke ɗaukar sojojin, duk da cewa ƙungiyoyin da ke horas da ƴan sa kai na VDP kan kare hakkin bil’adama, sun dakatar da duk wasu aikace-aikace a ƙasar.
A cewar ƙungiyar ta Human Rights Watch, hakan na sake jefa shakku kan yadda gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso za ta iya magance matsalar cin zarafin da dakarunta da aikata wa, wanda daga tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, fararen hula dubu 1 da ɗari 8 suka yi asarar rayukansu.
Credit: Source link
Comments are closed.