A yau lahadi,jam’ar ƙasar Guinea Bissau ke kaɗa kuri’ar raba gardama kan sauyin tsarin mulki zuwa tsarin shugaban kasa mai karfi iko don maye gurbin tsarin da ake da shi mai baiwa majalisa iko a baya.Muhimmin mataki ne a wanan ƙasa da sojoji ke rike da ita tun bayan juyin mulki da ya kawar da tsoffuwar gwamnati.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Minti 2 Lokacin karatu
Bayan Zimbabwe, Guinea, Togo, Uganda, da Chadi a cikin ‘yan shekarun nan, wannan shine sabon misali na wata ƙasa ta Afirka da ke neman gyara kundin tsarin mulkinta don tsawaita wa’adin shugabancin kasa,takaita shekaru, ko karfafa ikon bangaren zartarwa.
‘Yan adawa sun yi kira da a kauracewa kuri’ar raba gardama ta yau alahadi, musamman jam’iyyar PAIGC, jam’iyyar tarihi da ta jagoranci ƙasar zuwa ƴancin kai a shekarar 1974.
Jam’iyyar ta PAIGC ta yi Allah wadai da kuri’ar raba gardama a matsayin wadda aka gudanar “a cikin yanayi na takaita ‘yancin jama’a,” ganin yanayin siyasa mai tsauri da kasar ke ciki.
Shugaban gwamnatin rikon kwarya kuma shugaban sauyin, Janar Horta N’Tam, ya kaɗa ƙuri’a a unguwarsa a yau lahadi,ya kuma yi amfani da hakan wajen aikewa da kira ga matasa da su fito da yawa don kaɗa ƙuri’a.
“Abin da muke nema bayan wannan kuri’ar raba gardama shi ne a bai wa duk wanda ya lashe zaɓen na gaba damar kammala wa’adinsa cikin kwanciyar hankali.
A wani taron manema labarai, Idrissa Djalo, babban sakataren hukumar zabe ta kasa (CNE), ya bayyana gamsuwarsa da cewa “ba a bayar da rahoton rikici ko wata matsala dangane da zaɓen na yau lahadi ba.
Jama’a sun fito,wanda tamkar sako ne na cewa mutan ƙasar na goyon bayan wannan shiri.
A babban birnin kasar, Bissau, bayan fara aiki a hankali saboda ruwan sama mai karfi, masu kada kuri’a sun yi tururuwa zuwa rumfunan zabe da dama da kamfanin dillancin labarai na AFP ya ziyarta da tsakar rana.
Manufar hukumomin riƙon ƙwarya ita ce daidaita cibiyoyin kafin zaɓen shugaban ƙasa.
N’djamba Seide, wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya yi hira da shi yayin da yake barin wata rumfar zaɓe a Bissau, ya ce yana da “ƙwarin gwiwar zuwa ya kaɗa ƙuri’a” don “kawo canje-canje ga Kundin Tsarin Mulkin ƙasar” da “canza” abin da “koyaushe ke haifar da matsaloli a wannan ƙasar.”
Credit: Source link