An samu ɓarkewar cutar Mashaƙo ko kuma Diphtheria a turance a Senegal, inda mutane tara suka mutu, yayin da aka tabbatar da cewa mutane 79 zuwa yanzu sun kamu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
Bayanai sun ce cutar ta bazu zuwa yankuna 11 daga cikin 14 na ƙasar, musamman yankin Kédougou da ke gabashin Senegal.
Hukumomin lafiya sun buƙaci jama’a da su gaggauta zuwa asibiti da zarar sun fara fuskantar zazzabi, tare da tabbatar da cewa sun yi allurar rigakafin cutar.
An samu rahoton farko na cutar diphtheria a Senegal a ranar 30 ga watan Yuli, a yankin Kédougou.
Tun shekarar 2025 zuwa yanzu Mali, Mauritania da Guinea ke shan fama da cutar ta diphtheria, lamarin da ka iya zama sanadin shigowar cutar Senegal.
Rashin isasshen alluran rigakafi na daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen yaɗuwar cutar.
Duk da cewa kaso 88 cikin 100 na al’ummar Senegal na samun allurar rigakafi, cutar mai saurin yaɗuwa na ci gaba da kama yara, musamman waɗanda basu yi rigakafin ba.
Dr. Jean-Pierre Diallo, wanda ke jagorantar yaƙi da cutar a Ma’aikatar Lafiya, ya ce abin da ake fuskanta yanzu tamkar wani yaki ne lafiya ne, yana mai cewa kawo yanzu an gano mutane 249 da ake zargin sun kamu da cutar.
Bayan Kédougou, yankunan Dakar da Thiès ne suka fi fuskantar matsalar, kasancewar su ne yankunan da suka fi yawan jama’a a Senegal.
Credit: Source link