- Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta katse hulɗar diflomasiyya da Faransa, tana zargin ƙasar da yin abin da ya saba wa muradun ƙasarta
- Hakan ya biyo bayan tabarbarewar dangantaka tun bayan da Kyaftin Ibrahim Traoré ya karɓi mulki a juyin mulkin shekarar 2022
- Duk da katse hulɗar diflomasiyya, gwamnatin Burkina Faso ta ce dangantakar tarihi da zamantakewa tsakanin al’ummomin ƙasashen biyu za ta ci gaba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ouagadougou, Burkina Faso – Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta sanar da katse hulɗar diflomasiyya da Faransa.
Kasar da ke karkashin mulki soja tana zargin Paris da ci gaba da aikata abubuwan da suka saba wa muradun ƙasar.
Source: Getty Images
Dangantaka tsakanin Burkina Faso da tsohuwar ƙasar mulkin mallakarta ta ƙara tsami bayan Kyaftin Ibrahim Traoré ya karɓi mulki ta hanyar juyin mulki a shekarar 2022 tare da rungumar manufofin adawa da ƙasashen Yamma.
Hakan na cikin sanarwar da aka watsa ta talabijin wanda ministan sadarwa Pingdwendé Gilbert Ouédraogo ya yi jawabi, cewar BBC News.
Ministan ya zargi Faransa da ci gaba da katsalandan a harkokin ƙasar tare da nuna burin sabon mulkin mallaka.
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta bayyana matakin a matsayin na ƙiyayya kuma marar tushe, tana mai cewa hakan na nuna gwamnatin Burkina Faso tana ɗaukar wata hanya mai tayar da hankali.
Faransa ta kuma buƙaci ‘yan ƙasarta da ke zaune a Burkina Faso su ƙara taka-tsantsan saboda sauyin da aka samu a dangantakar ƙasashen biyu.
Burkina Faso, kamar maƙwabciyarta Mali, ta shafe fiye da shekara goma tana yaƙi da masu tayar da ƙayar baya, inda dakarun Faransa suka kasance suna taimakawa a yankin.
Bayan hawansa mulki, Kyaftin Traoré ya kori sojojin Faransa daga ƙasar, yayin da gwamnatinsa ta zargi Faransa da wata ɓoyayyar manufa tare da ƙarfafa alaƙa da China da Rasha.
Sabuwar sanarwar ta ce babu sauran yanayin mutunta juna tsakanin ƙasashen biyu, tana kuma zargin Faransa da goyon bayan ƙungiyoyin da ke neman tayar da zaune tsaye da kuma ware Burkina Faso a duniya.
Sai dai gwamnatin ta jaddada cewa katse hulɗar diflomasiyya ya shafi alaƙar hukumomi ne kawai, ba zai shafi dangantakar tarihi, al’adu, zamantakewa da bil’adama tsakanin al’ummomin Burkina Faso da Faransa ba.
Gwamnatin mulkin soja ta yi alkawarin mayar da mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 2024, amma daga baya ta fasa wannan alkawari tare da rushe jam’iyyun siyasa a watan Janairun bana.
A watan Janairun 2025, Burkina Faso tare da Mali da Nijar sun fice daga ECOWAS, inda suka kafa sabuwar ƙungiya mai suna Alliance of the Sahel States.
Faransa ba ta da jakada a Burkina Faso tun watan Janairun 2023, sannan a shekarar 2024 ƙasar ta kori jami’an diflomasiyyar Faransa uku bisa zargin aikata ayyukan tayar da zaune tsaye, zargin da Faransa ta musanta.
Burkina Faso ta dakatar da wasu gidajen jaridu
A baya, an ji cewa kasar Burkina Faso ta sanar da dakatar da manyan gidajen rediyon BBC da VOA daga watsa labarai a kasar.
An ruwaito cewa sanarwar ta fito ne daga ofishin sojojin da ke mulkin kasar a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilun 2024.
A cikin sanarwar sojojin sun bayyana dalilan da suka sa dakatarwar tare da fadin lokacin da za sujanye ta.
Asali: Legit.ng
Credit: Source link

