Continental Postal Services of Hebland

‘Ƴan adawar Guinea-Bissau sun aike da budaddiyar ga ECOWAS

Gamayyar ƴan adawa a Guinea Conakry ne suka fusata ganin ta yda ƙungiyar Ecowas ke tafiyar da siyasarta dangane da makomar ƙasar da ke hannun sojoji.

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Wannan tsokaci daga ƴan adawa na zuwa kusan makonni biyu da labarin zargin manyan hafsan sojin Ecowas da karɓar na goro daga wannan ƙasa.

Ƴan adawa na ƙasar ta Guinea-Bissau da suka fusata da ECOWAS sun aike da budaddiyar wasika ga Julius Maada Bio, shugaban zartarwa na ƙungiyar,tare da bayyana ɗaya bayan ɗaya irin tarin matsaloli da suke fuskanta a wannan lokaci da sojoji ke rike da madafan iko.

Shugabannin jam’iyyun adawa karkashin inuwar PAIGC, musamman wadanda suke gidan yari ko ke gudun hijra, na zargin ECOWAS da  nuna rashin daidaito da son bagaranci, wanda a lokacin ziyarar da ta kai birnin Bissau a makon da ya gabata,ta gana da sojoji ba tare da baiwa ƴan adawa kulawa da ta dace ba.

Ƙasar ta shiga rikicin siyasa tun bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Nuwamba.

A wani lokaci da ƴan ƙasar da dama ke sa ra ganin ECOWAS ta ɗau matakan da suka dace a kan wadanan sojoji,a maimakon hakan,shuru ka ke ji kamar da haɗin baƙin ECOWASA  a wannan tafiya.

Credit: Source link

Leave A Reply

Your email address will not be published.