- Marubuci, Thomas Naadi and Favour Nunoo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga Accra
Ghana na cikin matsalar rashin lantarki mai tsanani da ke shafar baki ɗayan ƙasar.
Ana samar da lantarki ne a Ghana ta hanyar iskar gas, da ruwa, da man fetur, da kuma makamashi mai ɗorewa – kamar hasken rana.
A 2021, an samar da kashi 63 cikin 100 na wutar daga iskar gas, kashi 34 daga ruwan kogi, kashi 3 daga man fetur, da ƙasa da kashi 1 daga hasken rana, a cewar hukumar kula da makamashi ta duniya International Energy Agency (IEA).
Sai dai kuma a ‘yan shekarun da suka wuce, ƙasar ta ci gaba da dogaro da gas saboda ya fi sauƙin sarrafawa sama da ruwa.
A yanzu Ghana ba ta da isasshiyar hanyar samar da iskar gas ɗin a cikin gida, wadda za ta isa a samar da lantarkin, saboda haka dole ne sai an sayo daga ƙasashen waje.
Amma a cewar Benjamin Boakye, wani mai sharhi a cibiyar Africa Centre for Energy Policy, ƙasar ba ta da isassun kuɗin da za ta iya sayo gas ɗin don bai wa tashoshin lantarki.
“Babu kuɗin da za a sayo makamashin ba tare da yankewa ba, wannan ta sa ba mu iya kunna injinan da ke buƙatar man fetur,” in ji shi.
Yayin da baki ɗayan wutar da ake iya samu ba ta wuce 5100 MW ba, ƙarancin gas ɗin ya sa Ghana ba ta samun lantarkin da ta wuce 3100 MW daga cikin abin da ya kamata a samu. Wannan ko kusa ba zai isa a bai wa ‘yan ƙasa da kuma masana’antu ba.
Bugu da ƙari, rashin inganta kayayyakin aiki a sashen lantarkin ya taka rawa wajen ƙarancin wutar.
‘Dumsor’ ta dawo kenan?
Kalmar ‘dumsor’ da ke nufin ɗauke wutar lantarki a harshen Akan na ƙasar Ghana, an fara amfani da ita ne a 2015 lokacin da ƙasar ta shiga matsanancin ƙarancin lantarkin da ya shafi tattalin arzikinta.
Dawowar dumsor a wannan lokaci abu ne mai muni ga ‘yan ƙasar.
Amanda Ohene Asiedu na da shagon sayar da ƙanƙararrun kaya a Kasuwar Makola da ke tsakiyar birnin Accra, ciki har da kaji, da kifi, da naman shanu.
“Saboda ɗauke wuta na yi asarar kusan Gh6,000 (dala 400),” a cewarta, tana mai cewa hakan ta sa dole ta sallami ma’aikatanta biyu.
“Kayayyakinmu ba su yi ƙanƙarar da ta dace saboda ƙarancin wuta. Haka muka zubar da wasu daga ciki, musamman kaji.”
Michael, wani mazaunin Accra, ransa a ɓace yake game da ɗuke-ɗauken wutar, inda ya nemi mutane su fito zanga-zanga.
“Lamarin yana damu na sosai saboda ba ni da kuɗin sayen inji,” a cewarsa.
“Sai su ɗauke wuta tsawon awa 24, ko awa 12, kana gani kayanka na ruɓewa. Idan aka ɗauke wutar sai mutum ya ji kamar ba zai rayu ba saboda zafi.”
Masu sharhi na ganin idan har Ghana na son kawo ƙarshen matsalar, akwai buƙatar ta inganta sashen wutar, ta faɗaɗa hanyoyin samun makamashi, sannan ta guji dogaro a kan gas.
Me ya sa bashi ya dabaibaye sashen lantarki na Ghana?
Sashen lantarki na Ghana a dabaibaye yake da bashi mai yawa da ya taru tsawon shekaru, saboda kamfanin Electricity Company of Ghana (ECG) ya gaza karɓar kuɗaɗen da yake bi bashin kwastomominsa.
A 2015, an yi yunƙurin karɓar kuɗaɗen da ake bi ɗin ta hanyar ƙara haraji, amma ba a iya aiwatar da tsarin ba yadda ya dace .
Baya ga wannan, akwai kuma masu shan wutar ba bisa ƙa’ida ba – inda masu gidaje kan jona wutar ta bayan fage don kada su biya kuɗi – lamarin da ya sa kamfanonin rarraba wutar ba su iya karɓar kuɗaɗen da suka dace.
A cewar ECG, satar wutar kaɗai yana jawo masa asarar kusan dala miliyan 418.2.
Kamfanin lantarki na Ghana kan sayi wutar daga Ghana Grid Company (GRIDCo), da kuma wasu ‘yan kasuwa kamar Takoradi International Company (TICo), da Sunon Asogli Power Plant (TAQA).
Amma saboda ƙarancin kuɗi waɗannan kamfanonin da ke samar da wutar na bin ECG bashin kusan dala biliyan 1.2 na wutar da ya saya kuma ya rarraba.
Haka nan, Najeriya na bin ƙasar bashi na iskar gas ɗin da aka samar ta kamfanin West Africa Gas Pipeline Company Limted (WAPCo).
Gwamnatin Ghana na fatan taimaka wa kamfanin biyan bashin ta hanyar sabon harajin da aka ƙaddamar a 2015, amma hakan bai yiwu ba.
A lokaci guda kuma, tattalin arzikin Ghana ma ya yi rauni, inda a yanzu yake rayuwa da tallafin asusun ba da lamuni (IMF) na dala biliyan uku.
Kazalika, faɗuwar darajar kuɗin ƙasar ma ta ta’azzara lamarin, ta yadda darajar kuɗin cedi ta faɗi da kashi 8.63 cikin 100 a kan dalar Amurka tun daga watan Janairu.
Me gwamnati ke yi a kan matsalar?
A matsayin wani muhimmin yunƙuri na gyara matsalar, ECG ya katse wa gidaje da ma’aikatun da suka gaza biyan kuɗi wutarsu.
A watan da ya gabata ne aka katse wa majalisar dokokin ƙasar wuta kan bashin dala miliyan 1.8 da aka biyo ta. An mayar da wutar bayan ta biya wasu daga cikin kuɗin.
Kamfanin ya kuma yi gargaɗin cewa akwai asibitoci 91 da yake bi bashin dala miliyan 20 kuma ya ce suna cikin haɗarin katsewar wutar.
Yayin da kamfanin ke ci gaba da ɗora alhakin ƙarancin wutar a kan matsalolin cikin gida, ana ci gaba ɗauke lantarkin akai-akai.
Yanzu mutane na neman a samar da wani jadawali da zai dinga fayyace lokacin da za a ɗauke musu wuta kafin a ɗauke.
Yanzu haka ana ja’inja tsakanin kamfanin samar da lantarkin, GRIDCo, da kuma ECG mai dillancin wutar kan wanda zai ɗauki gabarar wannan jadawalin.
Sai dai masana na ganin cewa ya kamata a fi mayar da hankali wajen cefanar da sashen karɓar haraji don tabbatar da cewa an dawo da kuɗaɗen da aka rasa.
Gwamnatin Ghana kan kashe sama da dala biliyan ɗaya wajen cike giɓin kuɗin da aka rasa.
Idan har gwamnatin ba ta ci gaba da sayen mai da kuma daidaita cinikayyar gas tsakaninta da Najeriya ba, ɗauke-ɗauken wutar zai ci gaba tsawon watanni masu zuwa.
Amma fa kafin gwamnatin ta iya yin hakan, sai ta samo dala miliyan 400 don samar da tabbatacciyar lantarki.
Credit: Source link